1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Daure 'yan jarida hudu na Rasha

Zainab Mohammed Abubakar Anna Saraste, Grzegorz Szymanowski/SB
April 16, 2025

Ana ci gaba da martani dangane da yanke wa wasu 'yan jarida hudu na Rasha, ciki har da biyu da suka yi aiki da DW, hukuncin daurin shekaru biyar da rabi a gidan yari saboda zargin laifin tsattsauran ra'ayi.

Rasha | 'Yan jarida hudu na Rasha da aka dauke
'Yan jarida hudu na Rasha da aka daukeHoto: Yulia Morozova/REUTERS

 

Ana kallon wannan daurin na su a matsayin wani bangare ne na salon murkushe masu adawa da shugaba Vladimir Putin ke yi. Irin farmakin da mahukunta ke kai wa 'yan adawa da 'yan jarida masu zaman kansu da kuma mutanen da ke sukar Kremlin. An yanke wa wadannan ‘yan jarida hudu na Rasha hukuncin zaman gidan yari na shekaru 5 da rabi ne a wata kotu da ke birnin Moscow bayan da aka gurfanar da su tun a watan Oktoban shekarar da ta gabata, hukuncin da bai zo da mamaki ba.

Antonina Favorskaya da Sergei Karelin da Konstantin Gabov da kuma Artem Kriger, duk sun musanta kasancewa cikin kungiyar masu tsattsauran ra'ayi. Ana yi wa hukuncin kallon wani karin murkushe 'yancin fadin albarkacin baki.

Karin Bayani:Rasha ta yanke wa tsofaffin 'yan jaridar DW hukuncin dauri

Biyu daga cikin 'yan jarida hudu na Rasha da aka daukeHoto: uncredited/AP/picture alliance

Favorskaya da Kriger sun yi aiki a kamfanin SOTAvision mai zaman kansa na Rasha. Sergey Karelin  kuwa ya kasance mai daukar hoto da kana Konstantin Gabov dan jarida kuma Furodusa. Duk sun yi aiki wa kafofin yada labarun kasashen waje daga Rasha, ciki har da Deutsche Welle.

Babban daraktan kafar DW Peter Limbourg da ya bayyana goyon baya ga 'yan mutanen hudu, ya ce hukuncin da aka yanke musu na nufin, Rasha ta sake tabbatar da cewa ita ce kasar da ta yi watsi da doka. Gwamnatin Rasha tana yin duk abin da za ta iya don karkatar da gaskiya, tare da mayar da 'yan jarida masu hazaka kamar masu aikata laifuka.

'Yan jarida hudu na Rasha da aka daukeHoto: Igor Ivanko/Kommersant Photo/Sipa USA/picture alliance

Mai fafutukar kare hakkin al'umma na Memorial Rights Center da ke Rasha Sergei Davidis, ya ce ana tsananta musu ne saboda kwarewarsu a aikin jarida, wanda hakan ne ya sa ake daukar su a matsayin fursunonin siyasa. Yada duk wani labari da bai dace da mahukunta ba yana da hadari.

Mutane masu yawa ne suka jinjinawa 'yan jaridun hudu a matakin farko na shari'ar, wanda da dama daga cikin masu lura da al'amuran yau da kullum suka ce Kremlin ce ke tabbatar da sakamakon. Kuma sun kasance na baya-bayan nan da suka fuskanci hukuncin kotu, kuma kari ne a kan jerin sunayen 'yan adawa masu zaman kansu, da 'yan jarida masu zaman kansu, da kuma 'yan kasar Rasha da ke fadin ra'ayinsu na sukar gwamnati game a kan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.