Sake dawo takarar dan adawa
August 30, 2024Kotun kula da harkokin mulki ta kasar Tunisiya ta amince da bukatar daya daga cikin fitattun 'yan siyasar kasar Imed Daimi na saka sunansa a jerin 'yan takara a zaben shugaban kasar da aka tsara ranar 6 ga watan Oktoba mai zuwa.
Yanzu haka Imed Daimi ya zama mutum na uku da kotu a kasar ta ba da umurnin a mayar da sunansa daga cikin wadanda aka yi watsi da takardunsu na takara a zaben da ke tafe, inda tun farko aka mayar da sunayen Abdellatif Mekki da Mondher Znaidi.
Ana zargin hukumar zaben kasar ta Tunisiya da ke yankin arewacin Afirka da nuna rashin sanin makamar aiki gami da zama karen farautar bangaren zartaswa. Shi kansa Shugaba Kais Saied yana cikin yan takara wanda yake neman wa'adi na biyu na mulki, duk da zargin da ake masa na zama dan kama karya.