An fadada zaben kasar Zambiya
January 21, 2015Talla
Sakamakon farko na zaben shugaban kasar Zambiya ya nuna dan takaran jam'iyya mai mulki ta PF, Edgar Lungu ke kan gaba, yayin da aka fadada zaben na jiya Litinin zuwa yau Laraba, saboda ruwan sama da aka sheka ya janyo kasa kammala zaben na jiya.
Sakamakon mazabu 14 daga cikin 150 da aka samu ya nuna Edgar Lungu dan shekaru 58, ministan tsaro da shari'a ya shiga gaban Hakainde Hichilema dan shekaru 52 masanin tattalin tattalin arziki na jam'iyyar adawa ta UPND.
Mahukuntan kasar ta Zambiya sun tura jiragen sama masu saukan ungulu domin dauko akwatunan zabe. kasar tana da kimanin masu zaben milyan biyar daga cikin al'umar kasar milyan 15.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu