Najeriya: An gayyaci shugaban Izala
March 30, 2020Gwamnatin Jihar Filato ta mayar da martani game da matakin da shugaban majalisar malamai na Kungiyar Izala Najeriya Sheik Sani Yahaya Jinigr ya yi biyo bayan jagorar Sallar Juma'a da dandazon mutane fiye da 50 bayan ta dauki matakin hana yin haka a ko ina cikin fadin jihar.
Sakataren gwamnatin jihar Filato Farfesa Danladi Atu, ya ce gwamnatin jihar ba za ta amince da karya dokokin da aka kafa domin kare lafiyar al'umma ba sakamakon bullar wannan cuta ta Coronavirus.
Cikin martaninsa lokacin taron manema labarai da maraicen yau a Jos fadar gwmanatin ta Filato, sakataren gwamnatin ya ce jami'an tsaro sun gayyaci shugaban majalisar malamai na Kungiyar Izalar Sheikh Sani Yahaya Jingir domin ya bayyana dalilansa na shugabantar sallar Juma'a da mutane fiye da 50, kamar yadda doka ta amince a yi.
Kawo yanzu dai babu wasu cikkakun bayanai daga bangaren jami'an tsaro kan matakin gaiyyatar malamin don amsa tambayoyi.