An fara duba lafiyar Alexei Navalny a Jamus
August 22, 2020Talla
Kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA ya ce jirgin da ke dauke da Alexei Navalny ya sauka ne a filin jirgin sama na Tegel kuma kai tsaye aka wuce da shi asibiti inda yanzu haka likitoci ke duba lafiyarsa.
Gabannin isowarsa Jamus dai, Mr. Navalny ya kwanta a wani asibiti da ke birnin Omsk na yankin Siberiya inda aka yi ta kai ruwa rana kafin a bari a fice da shi daga birnin zuwa Berlin don samun kulawar likitoci.
Likitoci a Rasha dai sun ce zargin da ake yi na sanya masa guba a shayi ba shi da tushe balle makama domin kuwa gwaje-gwajen da aka yi masa ba su nuna alamun guba a tattare da shi ba yayin da magoya bayansa suka ce ba haka zance yake ba.