1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Gangamin adawa da Trump ya barke a biranen Amurka

October 18, 2025

Za a gudanar da fiye da taruka 2,700 a wannan rana ta Asabar a biranen Amurka, domin yin tir da manufofin gwamnatin shugaba Donald Trump.

Masu zanga-zangar adawa da Donald Trump a birnin New York
Masu zanga-zangar adawa da Donald Trump a birnin New YorkHoto: Shannon Stapleton/REUTERS

An kaddamar da gamgamin adawa da Donald Trump a sassa daban-daban na Amurka a Asabar din nan, kama daga birnin New York zuwa San Francisco, gangamin da magoya bayan shugaban suka bayyana a matsayin kiyayya ga Amurka.

Wadanda suka shirya gangamin da aka yi wa lakabi da 'No Kings' sun ce ana sa ran miliyoyin Amurkawa za su yi tattaki domin yin Allah wadai da karfin iko da shugaba Trump ke nunawa tun bayan dawowarsa kan madafun iko.

Fiye da taruka 2,700 ne ake shirin gudanarwa a wannan rana ta Asabar a manya da kananan birane na fadin Amurka, ciki kuwa har da kusa da gidan da Donald Trump ke hutun karshen mako wanda ke a jihar Florida.

Karin bayani: Baki miliyan daya sun fice daga Amurka saboda Trump

Wannan rana ta gangami dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Amurka ta gaza samar da kasafin kudi, yayin kuma da Donald Trump ya tura sojoji zuwa jihohin da ke karkashin gwamnonin jami'ayyar Democrat domin yaki da bakin haure da kuma masu aikata muggan laifuka.