1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara gudanar da taron G20

November 15, 2022

An fara gudanar da taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 a wannan Talatar a kasar Indonesiya, inda batun yakin Rasha a Ukraine ya mamaye zauren taron.

Taron G20 a kasar Indonesiya
Hoto: Christoph Soeder/dpa/picture alliance

A lokacin da yake jawabi, yayin bude taron, mai masaukin baki shuagaba Joko Widodo na Indonesiya ya bukaci shugabanin kasashe manbobin kungiyar da ke halartar taron da su kawo karshen yakin.

Shugaba Widodo ya ce babu makawa, akwai bukatar a hada kai wajen ceto duniya da ta fada cikin rikici kana akwai bukatar magance fadawa cikin yaki na cacar baka. Ya kara da cewa a kullum ana kara samun wadanda suke rasa rayukansu a Ukraine, baya ga tasirin da yakin ya yi kan makamashi da kuma abinci a duniya.