An fara jigilar Mahajjatan kasar Niger
October 1, 2012 A Jamhuriyar Niger an soma jigilar maniyatan kasar zuwa kasar sa'udiyya domin sabke faralin hajjin bana a cikin konciyar hankali da lumana. Kimanin maniyata dubu 15 yan kasar ta Niger ke sabke faralin aikin Hajjin na bana;a karfe hudu da rabi na yammacin yau ne jirgin farko ya tashi da maniyata 550. Mahajjatan sun fara tashi ne ranar Litinin daga babbar taashar jiragen sama na Diori Hamani da ke
a birnin Yamai.
"Jim kadan bayan tashin jirgin ministan cikin gida na kasar niger wanda
shine ke da nauyin shirya aikin hajji a kasar ta niger Mallam Abdu Labo
ya bayanna farin cikinsa da yanda aikin jigilar maniyatan ya soma.
Lalle yanda ku ka gani maniyatammu sun fara tafiya wannan murna ce
gare mu tunda dama mun ce daya ga wannan watan za a fara tafiya kuma
gashi Allah ya sa a yau mun cika shi;kenan a gare mu babban murna
ce.muna fatan kuma kingin da su ka yi saura suma allah ya kaisu lafiya
ya maido su lafiya.na biyuin sun ka tafi tunda yan kasa ne wajibi ne
su rokomma kasarmu Niger konciyar hankali da zaman lafiya."
Daruruwan musulmi dai ne maza da mata su ka sami nasarar kansacewa
daga cikin wanan jirgi na farko. Na kuma isa har a cikin jirgin,inda na
yi fira da wasu daga cikinsu inda su ka bayayna farin cikinsu da
fatansu ga kasarsu a albarkacin hajjin na bana.
"Alhamdu Lillah, na ji dadin wannan rana, yanda Allah Ubangiji ya
gwada mana wanna ranar Allah ya gwada ma kowa wannan ranar, Allah sa mu
yi Hajji mai kyau. Muna godiya ga Allah wanda ya nuna mana wannan ranar kuma za mu je mu roka ma kammu, mu roka ma kasarmu da duniya baki daya, Allah ya bada
zaman lafiya da konciyar hankali. Na godewa Allah domin wallahi bana tsammanin jirgi zai zo yau amma sai gashi jirgi ya zo, kuma akan lokaci, kuma gani cikin shi. Yau mi na ke so illah Allah ya sabke mu lafiya."
Za'a dai share kwanaki 10 ne ana aikin jigilar maniyatan kasar ta Niger.
Sai dai duk da irin wanann nasara da aka samu ta tashin jirgin farkon a
cikin tsanaki, wasu yan matsaloli da su ka kunno kai a gap da soma
tashin jirgin bayan da wasu maniyata su ka ki amincewa da su zamo
muharaman wasu matan maniyata kamar yanda kamfanononin aikin Hajjin su
ka tsara da farko. A yayin da a share daya jamian kutsum su ka yi
nasarar bankado sirrin wasu maniyatan da da su ka yi sarandan goro
da wasu sauran haramtaccin hajoji da su ke da niyyar isa fataucinsu
zuwa kasar mai tsarki.
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Umaru Aliyu