An fara kai agaji a tsibirin Solomon
April 3, 2007Talla
An fara kaiwa kayan agaji ga kauyukan da mabaliyar ruwa ta tsunami ta rutsa da su a tsibirin Solomon dake kudancin pacific.
Wani karamin jirgin ruwa dauke da kayaiyakin agajin gaggawa ya isa babban birnin lardin wato Gizo.
Wannan yanki dai yana a tazarar kilomita 40 daga inda girgizar kasar karkashin ruwa mai karfin 8.0 a maaunin richter.
Rahotanni sunce akalla mutane 20 suka rasa rayukansu dubbai kuma suka rasa gidajensu daga wannan balai daya shafi kauyuka da dama na tsibirin.