1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana jiran sanin yadda zabe ya kaya a jihohin Najeriya

March 18, 2023

Bayan kammala zaben jihohi a Najeriya, an fara harhada sakamako daga sassan kasar. Da ranar Asabar ne dai aka yi zaben gwamnoni da na 'yan majalisu kamar yadda aka tsara.

Hoto: Patrick Meinhardt/AFP

A jihar Kano mutane sun yi zaben gwamna da na ‘yan majalisun dokoki kamar yadda aka yi a sauran jihohin Najeriya. Bayanai sun nunar da cewa zaben ya gudana lafiya koda yake ana samun matsaloli a wasu wuraren. Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da nasa zaben har ma ya yi kira da a yi zaben lafiya kuma wanda duk ya sami nasara a ba shi.

Ya yi zaben sa a mazabarsa da ke Ganduje a karamar hukumar Dawakin Tofa, ya kuma ja hankalin shugabanni da su zamo masu yarda da kaddara tare da kauce wa duk wani yunkuri da ka iya kawo yamutsi. Gwamna Ganduje ya kuma yaba da yadda zaben ke gudana.

Sai dai an sami tangardar na'urar B-VAS mai tantance masu zabe duk da ikirarin hukumar zabe na saita tsarin aikinta ta yadda za ta kunshi bayanan masu zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin inda mutane da dama ba su yi zabe ba. Sannan an samu 'yan hatsaniya jifa-jifa a tsakanin magoya bayanan APC da kuma NNPP saboda yadda bangarorin suka ci buri.

Hoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

A jihohin Katsina da Zamfara ma an kada kuri'u a zaben na gwamna da na ‘yan majalisun inda gwamnan jihar Bello Matawalle wanda shi ne dantakarar jam'iyyar APC ya bayyana gamsuwarsa kan yadda zaben ya gudana musamman tsarin hukumar zabe da ma yadda masu kada kuri'a suka yi zaben cikin lumana.

A jihohin Borno da Yobe an gudanar zaben ba tare da wata matsala ba in banda rashin fitan mutane a zabukan saboda matsaloli na rashin kudi da karancin man Fetur da ake fama da su, sannan wasu kuma sun yanke kauna saboda abin da suke zargin ya faru a zaben kasa da ya gabata.

An samu karancin fitowar jama’a a galibin wuraren da aka gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisun dokoki a jihohin Neja da Kogi. Sai dai ba a a fuskanci wani tashin hankali ba, kuma jami’an zabe sun fita a kan lokaci.

Hoto: MICHELE SPATARI/AFP

Daga yankin kudancin Njaeriyar musamman a yankin Ogoni kuwa, an samu rahotannin samun yamutsi inda 'yan bindigar siyasa suka yi ta wartar kayayyakin zabe. A wasu yankuna na jihar Rivers ma an samu bayanan rashin fitowar masu zabe kamar yadda aka gani a lokacin zaben kasa ba. Haka ma bayanai sun nunar da cewa kayayyakin zabe ba su iso rumfunan zabe a kan lokaci ba.

A jihar Legas kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dage zabe a mazabu 10 da ke jihar. Kwamishinan hukumar zabe a jihar, Olusegun Agbaje ya ce ma'aikatan wucin gadin da ke aiki a yankunan da abin ya shafa sun ki gudanar da aikinsu saboda matsaloli da suka gamu da suka ci karo da su yayin zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 25 ga watan jiya.