1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An fara kirga kuri'un zaben shugaban kasa a Ghana

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 8, 2024

Ghana da ke da tarihin gudanar da zabe cikin lumana a Afirka, to sai dai rundunar 'yan sandan kasar ta tabbatar da mutuwar mutane biyu sakamakon harbin bindiga.

Zaben Ghana
Hoto: Julius Mortsi/ZUMAPRESS/picture alliance

An fara kirga kuri'u a kasar Ghana, bayan zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki da aka gudanar ranar Asabar, inda mataimakin shugaban kasa Mahamudu Bawumia na jam'iyya mai muki ta NPP ke fafatawa da tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama na babban jam'iyyar adawa ta NDC.

Karin bayani:Ana tattara sakamakon zabe a Ghana

Ghana wadda ke da tarihin gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana a nahiyar Afirka, to sai dai a wannan karo rundunar 'yan sandan kasar ta tabbatar da mutuwar mutane biyu sakamakon harbin bindiga.

Karin bayani:Rawar matasa a babban zaben Ghana

Tabarbarewar tattalin arziki na daya daga cikin tarin matsalolin da suka addabi Ghana a 'yan shekarun nan duk kuwa da arzikin Gwal da Cocoa da ubangiji ya huwace mata, inda yanzu haka take fama da bashin biliyoyin daloli daga asusun bada lamuni na duniya IMF.