An fara kwashe 'yan Sudan ta Kudu daga Sudan
May 14, 2012Jirgin farko na mutanen ya bar Sudan da sanyin safiyar yau inda ya sauka da mutane ɗari da sittin da shidda a filin jirgin saman Juba, babban birnin Sudan ta Kudu.
Da ya ke jawabi game da wannan batu, ministan da ke kula da sha'anin jin daɗin al'umma Joseph Lual Acuil wanda ya isa filin jirgin saman don tarar jama'ar da su ka sauka ya bayyana jin dadinsa game da isar mutanen gida.
Wannan kason da su ka sauka a yau dai na daga cikin mutane dubu sha biyar ɗin da yanzu haka za a kwashe daga Sudan zuwa Sudan ta Kudu.
Kwashe al'ummar dai ta biyo bayan sanya wa'adin ranar ashirin ga wannan watan da mu ke ciki don 'yan kasar ta Sudan ta Kudu su fice daga Sudan domin ita Sudan na daukar zaman 'yan Sudan ta Kudun a ƙasar ta a matsayin wata barazana ta tsaro.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Saleh Umar Saleh