1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriyar: Sauran jihohi sun fara rufe makarantu

March 1, 2021

Kamar sauran wasu jihohin arewacin Najeriya, ita ma gwamnatin Jihar Sakwato ta bayar da umurnin rufe makarantun kawana da ke wajen babban birnin jihar a wani mataki na tunkarar matsalar rashin tsaro.

Nigeria Kankara | Angriff auf Schule | Entführte Schulkinder
Hoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Daukar wannan mataki na rufe makarantun Sakandare na kwana da ke wajen birnin jihar ta Sakwato na zuwa ne jim kadan bayan wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro da kuma Ilimi a jihar, da gwaman jihar Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranta, abin da ya kai ga cimma matsaya ga daukar wannan mataki. Daukar wannan mataki dai bai rasa nasaba ne ga yadda ‘yan bindiga ke cigaba da kai farmaki ga dalibbai tare da yin  garkuwa da su a arewacin Najeriya, na baya-bayan nan shi ne na dalibban Jangebe da ke Jihar Zamfara abin da ke cigaba da razana iyayen dalibbai. Gwamantocin jihohi a arewacin Najeriya dai na cigaba da kargame makarantu  abin da wasu ke ganin wannan ai mika wuya ne ga ‘yan bindiga sabanin a hada kai don a yakesu.
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani