Omar al-Bashir ya gurafana gaban Kotu
August 19, 2019![Sudan Khartum Ex-Präsident Umar al-Baschir vor Gericht](https://static.dw.com/image/50078530_800.webp)
Talla
Sanye da fararen kaya irin na gargajiya, zaune cikin wani akurki na karfe da ke cikin kotun ta birnin Khartum, magoya bayan tsohon shugaban sun barke da kabbara a yayin da hukumar yan sanda ta bayyana cewa ya karbi kudi kudi daga kasar Saudiyya.
Masu bincike a kasar ta Sudan na zargin shugaba el-Bashir da karbar kudi da suka kai dalar Amirka miliyan 90 daga yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed ben Salmane
Omar el-Bashir wanda ke tsare a wani gidan yari da ke birnin Khartum, hukumar mulkin sojan kasar na zarginsa ne da tara makudan kudade fiye da dalar Amirka miliyan dari da 13 a yayin wani samame da suka kaddamar a gidansa, jim kadan bayan hambarar da shi daga madafan iko.