SiyasaArewacin Amurka
An fara shari'ar Donald Trump kan zargin bada toshiyar baki
April 22, 2024![Tsohon shugaban Amurka Donald Trump a wani zaman kotun Manhattan na Amurka](https://static.dw.com/image/68835925_800.webp)
Talla
Masu gabatar da kara suna can suna bayyana masa dalilan da suka sa kudaden da ya bai wa wata fitacciyar mai fina-finan batsa a matsayin toshiyar baki ya zama laifi da kuma karya doka.
Karin bayani: Donald Trump zai gurfana a gaban kotu
Donald Trump dai shi ne shugaban kasar Amurka na farko da ya ke fuskantar shari'a a gaban kotu kan wani babban laifi irin wannan; su ma lauyoyin Trump za su gabatar da nasu bayanan a gaban kotu domin kare shi daga laifin da tuni ya musanta.
Karin bayani: Kotun kolin Amurka ta bai wa Trump damar tsayawa takara
An yi zargin tsohon lauyan Trump Michael Cohen ne ya bada kudin dala $130,000 ga Stormy Daniels a matsayin toshiyar baki don kar ta fallasa a bin lalatar da ta shiga tsakaninta da Trump.