An fara shari'ar wata 'yar kungiyar 'yan Nazi a Jamus
May 6, 2013Wannan ƙungiya ta NSU mai ra'ayin kyamar baki da aka gano cikin bazata, wadda kuma ta riƙa gudanar da ayyukanta na tsawon fiye da shekaru 10 ba tare da an gane ba, ya tilasta wa Jamus ta amince cewa yanayin masu ra'ayin ta'addanci da kuma masu yaɗa aƙidun 'yan Nazi ya wuce yadda hukumomin suka zata tun farko.
Beate Zschaepe mai shekaru 38, ana zarginta da hannu wajen bindige Turkawa takwas da wani dan Girka guda ɗaya, da kuma wata Bajamushiya 'yar sanda a wasu garuruwan Jamus tsakanin shekarar 2000 da 2007 da kuma tayar da bama-bamai a yankunan baƙin da ke birnin Cologne da kuma fashi a bankuna 15, ana kuma kyautata zaton cewa mataimakanta biyu sun kashe kansu a shekarar 2011.
Andrea Titz ita ce mai magana da yawun kotun da ke sauraron wannan shari'an Titz:
"Wannan babbar shari'a ce wacce ta ƙunshi fannonin shari'a da dama. Amma idan ana ganin cewa zai buɗe hanyar warware sauran miyagun laifukan da aka tabka, waɗanda suka danganci wannan shari'a kada ma a sa rai".
Masu shigar da ƙara sun ce duk da cewa bata taɓa amfani da tsinin bindiga ba, Zschaepe ta taka muhimmiyar rawa a ƙungiyar ta NSU wajen daidaita lamura. Lokacin shari'ar lauyoyin da ke kare ta sun ƙalubalanci mai shari'ar saboda banbanci, bayan da ya sanya jami'an tsaro su binciki wasu daga cikin waɗanda suka zo shari'ar.
Mahimmancin wannan shari'a
Wannan shari'a dai na da rassa daban-daban waɗanda suka danganci tarihi, zamantakewa da siyasa, kuma wannan shari'a ta NSU, ita ce ɗaya daga cikin mafi mahimmanci, tun bayan yaƙin duniya na biyu.
A wajen kotun wanda 'yan sanda 500 suka zagaye, al'ummomin Turkawa da Jamusawa da masu zanga-zangar nuna adawa da wariya sun riƙe takardu waɗanda ke cewa Zschaepe sai kin biya duk laifukan da kika tabka.
Wannan shari'a dai ta girgiza ƙasar da ake ganin ta yi koyi da abubuwan da suka faru da ita a shekarun baya, abunda kuma ya sake buɗe mahawara kan ko ya kamata Jamus ta ƙara ɗaukan matakai wajen daƙile ƙyamar baƙi musamman daga wurin masu ra'ayin riƙau. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ba da tabbacin cewa gwamnatinta zata yi iya ƙoƙarinta:
Matakan da gwamnatin Tarayya za ta ɗauka
"A matsayi na na shugabar gwamnatin tarayya, ina mai alkawarta muku cewa za mu yi duk iya kokarin warware wannan batu na kashe kashe. Za mu gano dukkan wadanda ke da hannu a ciki kana kuma a hukunta su gaban shari'a."
Majalisar dokokin Jamus tana gudanar da bincike dan gano yadda jami'an tsaro suka gaza gano kashe-kashen su ma yaɗa bayanai duk da cewa suna da majiyoyi da ke da kusanci da waɗannan mutane Wolfgang Wenger shi ne mai magana da yawun 'yan sandan kuma ya bayyana matakan tsaron da suka ɗauka wajen shari'ar;
"Muna da ayyuka daban-daban muna sanya ido kan yadda abubuwa ke gudana kana kuma mu goyi bayan masu shari'an mu tabbatar da tsaro a kotu mu kuma kula da motar da za'a kawo wanda ake zargi, a yau mun raba mutane zuwa rukunnai har uku, mafi ƙanƙanci ya ƙunshi mutane biyu mafi yawa kuma 500."
Za'a sake sauraron ƙarar a shekarar 2014 inda ake sa ran iyalan Zschaepe waɗanda ta daɗe ba ta gani ba, za su kasance su bada shaida.
Mawallafiya : Pinado Abdu-Waba
Edita : Mohammad Nasiru Awal