Tattauna yarjejeniyar nukiliya
June 20, 2021Manyan jami'an kasashen duniya da a baya suka aminta da yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran sun koma kan teburin tattaunawa a birnin Vienna na kasar Austriya, domin ci gaba daga inda suka tsaya a kan matsayar da aka cimma a shekarar 2015, wacce tsohuwar gwamnatin Amirka, karkashin Donald Trump, ta yi watsi da ita.
Wannan shi ne karon farko da ake sake bude babin tun bayan wani lokaci. Enrique Mora mai wakiltar kungiyar tarayyar Turai wanda kuma ya jagoranci tattaunawar da ta gudana tsakanin kasashen Rasha da China da Jamus da Faransa da Birtaniya da ma ita kanta Iran din, ya shaidawa manema labarai cewa sun kama hanyar samun matsaya.
To sai dai wasu jami'an na nuna damuwarsu a game da sabon shugaban kasar da aka zaba a karshen wanna mako, wanda suka ce zai iya maida hannun agogo baya.