Majiyar tace tuni Sepp Blatter ya bayar da kai bori ya hau
September 25, 2015Talla
A yau ne a birin Zurich na kasar Switzerland aka fara tuhumar Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya wato Sepp Blatter abisa zarge-zargen cinhanci da karbar rashawa a hukumar gudanarwar kwalon kafar duniya.
Tun dai a ranar 27 ga watan mayun shekara ta 2015 hukumar FIFA ke bayar da hadin kai ga ofishin babban alkalin birnin Zurich tare da tattara muhimman bayanai ga ofishin.
A yayin da ofishin babban Antoney Janar yake fadawa manema rabarai a Zurich ya nunar da cewar an gudanar da bincike a ofishin shugaban hukumar kwallon kafar duniyar tare da yin awan gaba da muhimman takardu da ke da alaka da almundahanar kudaden hukumar.