An fara zaben shugaban kasa a Najeriya
March 28, 2015A Najeriya an fara tantance masu kada kuri'a a zaben shugaban kasa na na 'yan majalisun dokokin tarayya. Najeriya mai yawan al'umma fiye da miliyan 170, tana da yawan wadanda suka yi rajistar zabe kimanin miliyan 70. A zaben na wannan Asabar dai shugaba mai ci Goodluck Jonathan da ke neman wa'adin mulki na biyu, yana fuskantar babban kalubale daga abokin hamaiya kuma dan takarar jam'iyyar adawa ta APC, Muhammadu Buhari. Ayyukan tarzoma na masu ta da kayar baya na kungiyar Boko Haram sun dabaibaye zaben. Saboda dalilan rashin tsaron ne ma aka dage zaben daga ranar 14 ga watan Fabrairu zuwa 28 ga watan nan na Maris.
Duk da cewa an shirya zabukan na shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin tarayya, a wannan Asabar amma a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriyar, hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta soke zaben 'yan majalisar wakilan tarayya saboda rashin samun kayan aiki. Wakiliyarmu a Jigawa Zainab Rabo Ringim ta labarto mana cewa kawo yanzu hukumar ba ta sanya ranar gudanar da zaben 'yan majalisar wakilan a Jigawa ba, amma jami'inta ya ce watakila a hada shi da zaben gwamnoni da zai gudana nan da makonni biyu masu zuwa.