Rasha: Zaben 'yan majalisar dokoki
September 17, 2021Talla
Shugaba Vladimir Poutine ya yi kira ga 'yan kasar masu zabe da su kasance masu kishin kasa da zabar cancanta a wani sakon bidiyonsa da aka wallafa a shafukan sadarwa na gwamnatin kasar. Kakakin fadar gwamnatin Rasha, ya ce Shugaba Poutine zai kada tasa kuri'ar ne ta hanyar sadarwa, duba da yadda ayake ci gaba da killace kansa bayan da aka samu wani na kusa da shi ya kamu da cutar corona.
Ana shi bangare jagoran adawar kasar Alaxi Navalny ya yi kira ga magoyya bayansa da su kada kuri'a da niyar kawo sauyi a majalisar. Sai dai ko baya ga zaben 'yan majalisar dokokin ana kuma gabatar da zabukan yankuna da na kananamn hukumomi wanda ake dakon sakamakonsu a wannan Lahadi.