An fidda sunayen yan takara a Iran
May 22, 2013A ƙasar Iran hukumar tantace yan takaran shugaban ƙasa ta fidda sunayen mutane takwas da za su shiga takaran shugaban ƙasa a zaben wata mai zuwa. Daga cikin sunayen da aka amince musu shiga takara harda Saeed Jalili, wanda yanzu haka shine sakataren tsaron ƙasar Iran, kana shine ke wakiltar kasar Iran a tattaunawar nukilya da ta ke yi da ƙasashen yamma. Wasu da aka soke sunayensu harda tsohon shugaban ƙasar Hashemi Rafsanjani da kuma wani na hannun daman shugaban ƙasar Iran Ahmadinejad wato Esfandiar Rahim Mashaei. Don haka shugaban ƙasar ta Iran Ahmadinejad, yace zai sake tattaunawa da shugaban addinin ƙasar Ayatollah Ali Khamenei bisa soke sunan abokin nasa. Koda yake akwai dan uwan shugaba Ahmadinejad, wato Wavud Ahmadinejad wanda ya tsaya takaraqn shugaban ƙasa, amma tuni shugaba Mahmud Ahmadinejad yace zai goyi bayan shugaban ma'aikatar fadarsa a yanzu haka wato Esfandiar Rahim Mashaei. A ranar 14 ga watan juni mai tsayawa ne dai za a gudanar da zaben shugaban ƙasar ta Iran.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu