1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na yi taka tsan-tsan wajen sayar da makamai

Werkhäuser, Nina, Conrad, Naomi YB
February 27, 2019

Jamus na alfahari da taka tsan-tsan a tsare-tsarenta na fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, musamman batu na sayar da makamai ga kasashe da suka tsinci kai a yanayi na yaki.

DW Exclusive Deutsche Waffen in Jemen SPERRFRIST 26.02.2019 20 Uhr IDEX Waffenmesse
Hoto: DW/T. Hasel

Wani aikin binciken kwa-kwaf irin na 'yan jarida kan makamai da fasahar Jamus mai lakabin ''GermanArms'' ya gano cewa amfani da makaman da aka kera a Jamus a yakin da ake yi a Yemen ya zarce yadda aka yi tunani tun da fari, sojoji na Daular Larabawa da sojojin Saudiyya na amfani da makaman da aka kera a Jamus da ma fasahar kasar wajen aiyukan sojoji ta sama da kasa da ruwa a yakin Yemen.

Ministan tattalin arziki na Jamus Peter Altmaier ya ce ba shi da masaniya cewar Jamus na sayar da makamai zuwa Yemen

Hoto: EPA-EFE/REX/Shutterstock/N. Almahboobi

Aikin binciken na ''GermanArms'' da hadin gwiwar Deutsche Welle da wasu kafafan yada labarai na Jamus da suka hada da gungun kafofin yada labarai na Bayerischer Rundfunk da mujallar Stern Magazine da hadakar masu yada labarai masu zaman kansu na Lighthouse Report a Holland da masu binciken kwa-kwaf kan lamuran yaki da take hakkin bil Adama na Bellincat. 
Wakilai na gwamnatin Jamus dai sun ki amincewa da wannan zargi da ake wa kasar na cewa ana amfani da makaman da Jamus ta kera a yakin Yemen kamar yadda Peter Altmaier ministan tattalin arziki yayin taron koli na tsaro a Munich ke cewa:

''Bani da masaniya kan wannan batu, mun sani abin da muka gindaya a sharadinmu na hadaka, muna da ka'ida kan abin da ya shafi fitar da makamai, amma a ce Jamus na fitar da makamai kuma da sanin cewa kasar da aka kai na yaki kai tsaye wannan shi ne abin da ban sani ba.''