An gabatar da sakamakon binciken gawar Sankara
October 13, 2015A Burkina Faso a wannan Talata alkalin da ke bincike kan musabbabin mutuwar Thomas Sankara ya bayyana sakamakon farko na binciken da aka gudanar a kan gawar miragayin da aka tono. Sakamakon binciken da ya nunar da cewa gawar marigayin na cike da harsasai.
Sai dai Ambroise Farama daya daga cikin lauyoyin tsohon shugaban kasar ta Burkina ya ce sai an gudanar da gwajin kwayoyin halitta na ADN ne a nan gaba za a tantance in har gawar Thomas Sankara din ce ake gudanar da binciken a kanta ko kuma a a. .
Amma tuni kuma hukumomin shari'ar kasar suka dakatar da mutane takwas zuwa tara daga cikin har da sojoji mambobin tsohuwar rundunar tsaron lafiyar tsohon shugaban kasar Balise Compaore wato RSP,
A shekarar 1987 ne dai sojoji suka hallaka Shugaban Thomas Sankara a lokacin wani juyin milkin da suka yi wa gwamnatinsa.