1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanciMali

Mali: Tsageru za su bar kasar ta huta?

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 29, 2026

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa ta Amnesty, ta tabbatar da samun shaida kan yadda tsageru suke aikata laifukan yaki a kasar Mali da ke yankin yamamcin Afirka.

Mali | Kidal | 2026 | Abzinawa | Azawad Liberation Front
Mayakan tawayen Abzinawa sun takurawa MaliHoto: AFP

Kungiyar ta Amnesty International ta ce, ranar 18 ga wannan Yulin 2026 an kashe kimanin sojoji nMali 50 a lokacin da suke tafiya cikin wata tawaga. Ana zargin 'yan awaren Abzinawada kungiyoyin jihadi da aikata laifukan cikin yankin arewacin kasar.

Akwai dai hotunan bidiyo na yadda mayakan 'yan tawayen ke cin-zarafin mutanen da ba su dauke da makamai, inda ita kanta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci bincikekan halin da ake ciki a Malin. Mali na karkashin gwamnatin mulkin soja, tun bayan juyin mulkin shekara ta 2020 da na 2021.