An gana tsakanin Putin da Bush gabanin fara taron kolin kungiyar G-8
July 15, 2006Talla
Sa´o´i kalilan gabanin fara taron kolin kungiyar G8 ta kasashen da suka fi arzikin masana´antu a duniya, an yi wata ganawa tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amirka GWB a birnin St. Petersburg. Shugabannin biyu sun tattauna akan dangantaka tsakanin kasashen su. Hakazalika sun yi kuma musayar ra´ayoyi game da rikicin yankin GTT, da fito na fito da ake yi akan shirin nukiliyar Iran da kuma KTA. Wakilin gidan radiyon DW a birnin St. Petersburg Shaye Hoobanoff ya rawaito cewa shugabannin biyu sun kasa cimma wata yarjejeniya da zata share fagen shigar da Rasha cikin kungiyar cinikaiya ta duniya. A yau din nan ne ake fara taron yini 3 na kungiyar ta G-8, inda ake sa ran cewa shugabanni zasu samar da matsayi na bai daya akan rikicin na GTT. Sannan zasu kuma tattauna game da shirin nukiliyar Iran da gwajin makamai masu linzami da KTA ta yi. Shugabannin zasu kuma shawarta akan samar da makamashi a duniya baki daya.