1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu gawar bakin haure a Italiya

Abdul-raheem Hassan
July 24, 2022

Jiragen ruwan Italiya sun gano gawar mutane biyar da suka mutu a lokacin da suke kokarin tsallaka tekun Bahar Rum a cikin jiragen ruwa marasa inganci.

Wasu 'yan ci rani a cikin jirgin ruwa
Hoto: Joan Mateu/AP/picture alliance

Masu binciken sun ceto mutane 674 a cikin wani kwale-kwalen kamun kifi, jami'an tsaron gabar tekun sun ce wannan samamen daya ne daga cikin jerin ayyukan ceto da suka kaddamar a 'yan kwanakin nan.

Kungiyar agaji ta Jamus mai suna Sea-Watch, ta ceto bakin haure 444 da suke kokarin tsallakawa tekun Bahar Rum a kwale-kwalen 'yan fasa-kwauri, a cewar jami'an agajin, cikin mutane da aka ceto har da mata masu juna biyu da wani mutumin da ya ji rauni na kunar wuta a jikinsa.

Yanzu haka dai bincike ya nuna cewa adadin bakin haure daya bisa uku ne suka shiga kasar Italiya ta barauniyar hanya, idan aka kwatanta da wadan da suka shiga kasar a shekarar 2021.