1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano masu shigar da makaman da ke rura rikicin Sudan

February 9, 2012

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta zargi kasashe uku da alhakin shigar da makaman da ke rura rikicn Sudan

Soldaten der Rebellenorganisation «Sudanesische Befreiungsarmee» (SLA) patrouillieren in Muhujariya in Süden der sudanesischen Provinz Darfur (Archivfoto vom 25.04.2005). In der westsudanesischen Region Darfur spielt sich seit 2003 eine Tragödie ab. In dem Konflikt zwischen den rebellierenden Stämmen und der Zentralregierung starben bislang nach Angaben des Auswärtigen Amtes schätzungsweise 300 000 Menschen, über zwei Millionen Menschen mussten fliehen. Ein Friedensabkommen zwischen Khartum und der Rebellenorganisation «Sudanesische Befreiungsarmee» (SLA) vom Mai 2006 wurde bereits einen Monat später von den Aufständischen wieder annulliert. Jetzt hat Verteidigungsminister Jung (CDU) erklärt, Deutschland könnte im Rahmen eines UN-Mandats deutsche Soldaten auch nach Darfur entsenden. EPA/khaled el Fiqi (zu dpa 4462) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Masu tada kayar baya a yankin DafurHoto: picture alliance/dpa

Wani rahoto da kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta wallafa ya yi zargin cewa makamai daga kasashen China Rasha da Belarus na kara rura rikicin Sudan wanda ya kai tsawon shekaru tara yanzu.

A rahoton da ya fito da yammacin Laraba, kungiyar ta ce an gano makaman da ake sarrafawa a kasashen a yankin Dafur da sauran wuraren da ke fama da rikicin kusa da iyakar Sudan da Sudan ta Kudu.

Rahoton ya kuma bayyana yadda kasashen uku ke cigaba da baiwa kungiyoyin da ke tada kayar baya wadannan makamai, duk da cewa sun san fararen hula ake kai ma farmaki da su. Wadannan makamai dai sun hada da albarusai, da rokoki da kuma motocin yaki masu sulke

Kungiyar ta Amnesty ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta mayar da hankali wajen dakatar da shigar makaman wandannan yankunan.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita : Umaru Aliyu