An gargadi Najeriya kan yiwuwar kai hari
October 24, 2022Ba kasafai wadannan ofisoshin jakadancin Amirka da Birtaniya da Italiya ke fitar da sanarwa iri guda kuma a kan batu iri daya na yiwuwar kai hare-haren ta'adanci a Abujan babban birnin Najeriya ba. Saboda haka ne ta sanya tambayoyi a kan dalilin yin hakan da abin da suka gani. Hasali ma sun ja hankalin ‘yan kasarsu da ke Najeriyar da su yi taka-tsantsan a kan wuraren da suke zuwa, tare da daukar matakai. Sun ma zayyana wurare da dama da suka ce za'a iya kai harin ta'adanci a Abujan da suka hada da manyan shaguna da wuraren taron jama'a da wuraren ibada da hotal.
Wadannan jakadu sun ja hankali ga ‘yan asalin kasashensu da ke zaune a Najeriyar, amma sako ne da ke da amfani ga daukacin mutanen da ke zaune a Najeriyar da ma hukumomin tsaro wadanda za'a ce sun samu bayanai na sirri da sukan yi kukan rashin su na zama cikas.
Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriyar watau DSS ta mayar da martani a kan wannan sanarwa da ta sanya ‘yan Najeriya da dama ciki yanayi na zullumi. A sanarwar da jami'in yada labaru na hukumar Dr Peter Afunanya ya sanya wa hannu, hukumar DSS ta bukaci mazauna Abuja su kwantar da hankalinsu domin tana aiki da sauran hukumomin tsaro.
Akwai alamu daukan karin matakan tsaro a Abuja musamman a hanyoyin shiga birnin da ma wuraren gudanar da tarurruka.