Yariman Saudiyya yayi tsokaci kan kisan 'dan jarida
June 16, 2019![Dschamal Chaschukdschi](https://static.dw.com/image/45749790_800.webp)
Talla
Dangantaka tsakanin kasashen Saudiya da kuma Turkiya ta yi tsami tun bayan kisan gillar da aka yi wa 'dan jaridar a ofishinn jakadancin Saudiya da ke birnin Santanbul lamarin da ya janyowa Yarima Mohammaed bn Salman suka daga bangarori dabam-dabam.
Yariman dai ya bukaci duk wanda yake da gamsasshiyar shaida kan kisan Jamal Kashoggi da ya taimaka ya sanar da kotun Saudiya don a yi wa iyalan mamacin adalci. A baya dai hukumar CIA ta bayana cewar akwai yiwuwar yariman na Saudiya Mohammed Bn Salman ne ya bada umarnin kisan kan duk kuwa da cewar tuni masu gabatar da kara a Saudiya suka wanke shi bayan tsare mutane da dama a matsayin masu hannu a kisan dan jaridar.