1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gaza cimma matsaya tsakanin Amurka da Rasha a kan Ukraine

December 3, 2025

Duk da kwashe sa'o'i biyar ana tattaunawa tsakanin jami'an Amurka da na Rasha babu daidaito da aka cimma.

Duk da kwashe sa'o'i biyar ana tattaunawa tsakanin jami'an Amurka da na Rasha babu daidaito da aka cimma
Duk da kwashe sa'o'i biyar ana tattaunawa tsakanin jami'an Amurka da na Rasha babu daidaito da aka cimmaHoto: Kristina Kormilitsyna/Sputnik/AP Photo/picture alliance

Tattaunawar sa'o'i biyar tsakanin Shugaban Rasha Vladimir Putin da babban mai sasanta rikici na Shugaban Amurka Donald Trump ba ta haifar da wani muhimmin ci gaba ba a kokarin kulla yarjejeniyar zaman lafiya ta Ukraine.

Kakakin fadar Kremlin ya ce ganawar da aka yi a Moscow "mai ma'ana ce,” amma Rasha ba za ta amince da wani bangare na daftarin shirin zaman lafiyar ba.

NATO ta yaba wa yunkurin Trump na sulhu a Ukraine

Jakada na musamman ga shugaba Trump,Steve Witkoff, tare da surukin Trump din Jared Kushner, sun halarci tattaunawar ce da shugaban Rasha Vladimir Putin bayan makonni na ganawar diflomasiya da nufin kawo karshen yakin.

Ya zuwa yanzu tawagar Amurkan ba ta yi wani bayani ba tun bayan barin Moscow kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.

Rasha ta kaddamar da hare-hare a birnin Kyiv na Ukraine

A ranar Talata, Putin ya ce canje-canjen da Kyiv da kuma Turai suka yi a cikin daftarin zaman lafiya da Amurka gabatar ba sauye-sauye ne da za a amince da su ba, inda ya kara da cewa idan Turai “na son ta tunkari Rasha da yaki to a shirye take nan take.”

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW