Babu hanyar kai agaji ga 'yan Ukraine
March 7, 2022Talla
A rahoton da ta fidda a wannan Litinin, Majalisar Dinkin Duniya ta ce, daruruwan mutane da suka makale a kasar Ukraine na cikin wani hali na tsaka mai wuya, a yayin da aka toshe hanyar da za a isar musu da agajin da suke bukata na gaggawa.
Majalisar ta yi kira da a gaggauta bude hanyar da za ta kai ga mutanen da ke bukatar ficewa daga kasar da ma wadanda ke bukatar abinci da ruwa gami da magunguna.
Rasha ta sha alwashin bude hanya ga wadanda ke son isa kasar ko kuma zuwa kasar Belarus, matakin da mahukuntan na Ukraine suka ki aminta da shi.
A cewar ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da harkokin jin kai OCHA yanzu haka akwai manyan motoci dauke da kayayyakin agaji da suka kasa isa ga mabukata musamman asibitoci.