1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gaza kashe wutar rikici a Ukraine

February 2, 2014

Gwamnatin kasar Ukraine ta amince jagoran 'yan adawar nan da ya bayyana cewa an sace shi tare da azabtar da shi Dmytro Bulatov, ya bar kasar domin neman magani.

Hoto: picture alliance/AP Photo

Rahotanni sun bayyana cewa wata kotu ce a Kiev babban birnin kasar ta Ukraine ta amince Dmytro Bulatov ya fice daga kasar domin zuwa ya nemi magani, sakamakon raunukan da ya samu a yayin da aka sace shi tare da azabtar da shi.

A hannu guda kuma ana sa ran shugaban kasar ta Ukraine Viktor Yanukovych zai koma bakin aikinsa bayan da ya karbi hutun rashin lafiya sakamakon masassarar da ta make shi. Ofishin shugaban kasar ne dai ya sanar da cewa Yanukovych na fama da cutar da take da nasaba da numfashi, wanda hakan ya tilasta masa daukar hutun rashin lafiya a dai dai lokacin da 'yan adawar kasar ke ci gaba da gudanar da mummunar zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da ta rikide ta koma tashin hankali.

Firaministan kasar ta Ukraine da majalisar zartarwasa dai sun yi murabus, yayin da 'yan majalisar dokokin kasar suka amince da dokar yiwa 'yan adawar da aka kama afuwa da sharadin za su bar gine-ginen gwamnati da suka mamaye tare da dakatar da zanga-zangar, batun da 'yan adawar suka sa kafa suka yi fatali da shi.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu