An gaza sasanta Isra'ila da Hamas a Qatar
July 7, 2025
Talla
Majiyoyin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa bayan zaman farko na tattaunawar kai tsaye ta hanyar wakilai a Doha, wakilan Isra'ila sun nuna cewa ba su da cikakken izini ko iko da zai ba su damar kulla yarjejeniya da Hamas.
Kafar yada labaran BBC ta ruwaito cewa tattaunawar ta gudana ne a cikin gine-gine biyu dabam-dabam, kuma ta dauki kimanin sa'o'i uku da rabi.
An gudanar da tattaunawar ne ta hanyar masu shiga tsakani dagaQatar da Masar, amma ba a kai ga samar da wani ci-gaba ba. Amma ana sa ran za a ci gaba da tattaunawar nan ba da jimawa ba.