An girka komitin sulhunta rikicin siyasa a ƙasar Togo
April 23, 2006Jam´iyun siyasa a ƙasar Togo sun zaɓi shugaban jam´iyar CAR mai adawa, a matsayi shugaban komitin sulhu da sasanta rikicin siyasar ƙasa.
Ranar juma´a da ta gabata ne, yan siyasr da ƙungiyoyi masu zaman kansu , su ka koma tebrin shawarwari, da zumar warware ringinginmun siyasa, da su ka biwo bayan zaɓen shugaban ƙasa, da kashe- kahen jama´a, bayan mutuwar mirganyi Yasimbe Eyadema, ranar 5 ga watan Februaru, na shekara ta 2005.
Ɓangarorin na burin cimma matsa ɗaya, a game da batutun da su ka shafi kwaskwarima ga kunɗin zaɓe na ƙasa da shirye shiryen zaɓen yan majalisun dokoki da za a gudanar.
Hukumomin bada lamani na dunia da ƙungiyar gamaya turai,sun gitta shariɗin kyauttata harakokin siyasa, a ƙasar, kamin su bada taimakon kuɗaɗen tafiyar da ayyuka.