1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An girke tankokin yaƙi a birnin Homs na ƙasar Siriya

May 11, 2011

Gwamnatin Jamus ta nemi Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya da cewa a gurfanar da waɗanda ke da hannu a kashe kashen dake wakana a Siriyar.

Masu zanga-zanga a birnin HomsHoto: AP

Gwamnatin ƙasar Siriya ta girke tankokin yaƙi a unguwannin birnin Homs yayin da ƙasashen tarayyar Turai ke jaddada kira ga gamaiyar ƙasa da ƙasa da ta ɗauki matakai game da murƙushe masu zanga-zangar. Masu boren ƙyamar gwamnatin sun faɗawa gidan telebijin Al-Jazeera cewa an katse wutar lantar da layukan waya a birnin dake zama na uku mafi girma a ƙasar, inda kuma a makonnin nan aka yi ta gudanar da zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin shugaba Bashar al-Assad. Gwamnatin Jamus ta faɗawa Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya cewa ya kamata a gurfanar da waɗanda ke da hannu a kashe kashen dake wakana a Siriyar. Jakadan Jamus a MƊD Peter Wittig ya ce duniya ta kaɗu matuƙa game da tashe tashen hankulan da kuma matakan ba sani ba sabo da hukumomin Siriya ke ɗauka kan masu zanga-zangar lumana.

Ita ma a jawabin da ta yi a gaban majalisar dokokin tarayyar Turai dake birnin Strassburg, jami'ar kula da harkokin ƙetare ta EU Catherine Ashton kira ta yi ga gwamnatin shugaba Basahr al-Assad da ta sauya alƙibla dangane da matakan da take ɗauka kan masu adawa da ita.

"Damuwarmu a nan wurin da ma a cikin ƙungiyar EU tana akan mutanen Deera inda aka hana MDD shiga, da Banisa inda ake ci-gaba da murƙushe masu bore, da kuma Hama inda aka tura tankoki. Al'umar Siriya ba za su saduda ga tankoki ba. Muna kira ga gwamnati da ta canja alƙibla yanzu."

Ƙungiyoyin kare haƙin bil Adama sun cewa an kashe mutane kimanin 750 tun bayan fara zanga-zangar ƙin jinin gwamnati.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu