Bikin ranar ma'aikata a Najeriya
May 1, 2025
Dubban ma'aikata a dandalin Eagles Square da ke birnin Abuja suka yi bikin ranar ma'aikata a Najeriya. Duk da cewar dai sun dauki lokaci suna fareti ciki farin ciki da ma nishadi dai, bikin na bana na gudana ne a cikin halin matsi da karuwa ta talauci a tsakanin miliyoyin ma'aikatan Najeriya.
Tun a watan Yulin da ya shude ne dai gwamnatin kasar ta fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 har ya zuwa ranar yau dai kusan rabi na masu aiki a kasar na zaman jiran sabon albashin a cikin aljihunsu. Akalla wasu jihohi 20 da doriya dai har yanzu sun gaza kai wa ga biyan mafi karancin albashin.
Karin Bayani: Najeriya: Kalubalen sauyin sheka ga Jam'iyyar PDP
Kuma a Abuja dai ma'aikatan kanana na hukumomin birnin dai na cikin wani yajin aikin nuna bacin rai da kasa kai wa ya zuwa sauke nauyin. Sai a wannan mako ne dai ita kanta gwamnatin kasar ta kai ga cikon wani alkawari na biyan ma'aikatan Naira 35,000 domin rage radadin zare tallafin da ta yi a shekaru biyu da suka wuce.
Kuma masu aikin da suka aiyyana wasu jerin bukatu sabbabi har 12 dai basu boye bukatar wani sabon albashin ga gwamnatin kasar. Dr Muttaqa Yusha'u dai na zaman shugaba na gangami da ma waye kai na kungiyar NLC ta kwadagon Najeriyar, wanda ya nuna irin tasirin da ma'aikata suke da shi a matsayin kashin bayan al'umma.
A ka'ida ta dokar aiki dai sai bayan shekaru biyar ake iya kaiw a ya zuwa wani sabon kari bisa batun albashin. To sai dai kuma hauhawa ta farashin da ta mamaye daukacin lokacin sabon karin dai daga duk alamu na kara jefa tsarin aikin cikin barazana mai girma.
Dr Isa Abdullahi dai na zaman kwararre ga tattalin arziki. Kokari na inganta rayuwa ko kuma karin rudu cikin batun albashi, koma ya take shirin da ta kaya a tsakanin ma'aikatan da ke fadin da sauran sake, da gwamnatin da ke karatun babu, shi kansa shugaban kasar dai Bola Ahmed Tinubu ya kauce daga ambato batun albashin cikin jawabinsa ga masu kwadagon kasar.
Duk da cewar dai ya jaddadda burinsa na kyautata rayuwar yan aiki, jawabin na Shugaba Tinubu dai bai ce uffan ga jerin bukatun masu aikin Najeriya. Mohammed Mai Gari Dingyadi dai na zaman ministan kwadagon Najeriyar da kuma ya karanta jawabin na shugaba Tinubu. Kuma ya ce matsin na tattalin arziki ya koma ruwan daren da ke zaman game duniyar ma'aikata. Matsi na tattali na arziki da a yau ke zaman ruwan dare ya shafi kowane sashe na duniya. Kuma na gwada imanin shugabanni, amma kuma ba tare da kai wa ya zuwa karya gwiwa ba.
Ina sane da irin matsaloli na tattali na arzikin da al'ummar Najeriya ke fuskanta, wanda ya shafi matsaloli irin na tsadar rayuwa, da Rashin tsaro da yunwa da da hauhwa ta farashi da kuma matsa lambar biyan bukata ta iyali.
A bana dai Najeriya tana shirin kisan Naira Triliyan Takwas da doriya cikin sunan albashi da hakkoki na masu fansho na kasar. Adadin kuma da ya haura da kusan kaso 60 cikin 100 bisa kasafin ma'aikatan kasar na shekarar da ta shude. Adadin kuma da ke zaman rabin abun da gwamnatin take shiri na kashewa wajen biyan ruwan basukan ciki da ma wajen kasar a shekarar bana.