Bikin ranar Hausa ta duniya na shekarar bana
August 27, 2019Ranar 26 ga watan Agusta kowace shekara ce ake gudanar da bikin ranar harshen Hausa ta duniya. Albarkacin raya ranar ta bana, masana sun gabatar da makaloli a wani babban taron daliban Hausa na duniya da aka gabatar a jami'ar Bayero, da ke Kano inda suka bayyana bunkasar da harshen Hausa ke samu a duniya. Sai dai kuma har yanzu masana na kukan cewar tasirin Turawan mulkin mallaka na ci gaba da kawo cikas wajen harkar koyo da koyarwa da harshen Hausa, lamarin da ke zama kalubale ga harshen.
Binciken masana a fannin harshe ya dora harshen na Hausa a matsayin harshe na 11 da aka fi amfani da shi a duniya. Harshen da ke a matsayin na farko a duniyar shi ne harshen Mandarin sai Inglishi da ke biye masa baya yayin da harshen Hindu na kasar India ya zamo na uku. Harshen Hausa na ci gaba da burunkasa yana lamushe harsuna da dama wadanda galibinsu sun fuskanci yankan kunkurun Bala daga harshen na Hausa. To amma rashin mayar da kai ga Hausawa wajen koya wa masu tasowa kishin harshen na barazanar yi wa harshen na Hausa tashin tantabarun Hudu. Dan haka ne ma masana ke kira da a hada kai domin magance tarnaki da harshen ke fuskanta.
Sai dai a yayin Makala da ya gabatar yayin wannan gagarumin taro, farfesa Aliyu Bunza na jamiar usmanu Danfodio dake Sokoto ya bayyana cewar har yanzu dai da sauran rina a kaba, domin rashin amfani da harshen Hausa wajen koyar da dalibai a makarantu ya zama wani babban al'mari da ke zamar wa Hausawa tukin tuwon tulu.To amma cibiyar nazarin harshen Hausa da ke jami'ar Bayero ta ce ta fara kamo bakin zaren wannan matsala, har ma Farfesa Aliyu Mu'azu ya ce tuni sun fara samar da litattafan kimiyya da aka wallafa da harshen Hausa.
Aminu Suleman Goro shi ne shugaban kwmaitin ilimi na majalisar tarayyar Nigeria ya kuma halarci wannan taro yana mai alkawarin cewar za su duba yiwuwar shigar da litattafan cikin manhaja domin ganin an fitar da A'i daga Rogo. Yayin bikin farar kaza balbela an ce ba gayya ba ce, domin wasu Sinawa masu magana da harshen Mandarin wanda aka ce shi ne ya fi kowane yawan mutane a duniya kuma suke koyon Hausa sun halarci taron cikin murna da farin ciki tare da bayyana dalilinsu na karbar shahadar koyon harshen na Hausa.
Yayin wannan taro an nada Kwamared Nura Suleman a matsayin sarkin daliban Najeriya. Sai dai kuma babban abin da ke damun Hausawa shi ne matsalar rashin hadin kai a tsakanin juna domin shi kansa wannan taro na raya ranar yaren Hausa ta duniya, an yi farraku wajen gabatar da shi inda wasu masu taron suka gabatar da nasu taron daban a gidan dan Hausa da ke Kano.