An gudanar da ranar radiyoyi na duniya
February 13, 2014 Hukumar kula da ilimi da raya al'adu ta Majalissar Dinkin Duniya
wato UNESCO, ta kaddamar da ranar 13 ga watan ko wace Febrairu daga a bara, domin ta kasance ranar karrama gidajan radiyo a matsayinsu na kafofin yada labarai dama kuma kara karfafa huldar tsakanin gidajen radiyoyi na duniya. Wannan rana wacce ta yi daidai da ranar bude gidan radiyon MDD a shekara ta 1946, rana ce ta yin nazarin tasirin ayyuka gidajen radiyo a cikin rayuwar alumma, dama kuma kalubalen da su ke fuskanta a cikin tafiyar da aikinsu.
A lokacin kadawar guguwar demokradiyya ne a kasar ta Nijar a farkon
shekarun 1990 aka soma samun yaduwar sabbin gidajen radiyo masu zaman kansu a kasar, wacce har ya zuwa wanann lokaci na mallakar
gidan radiyo daya ne tilo na gwamnati wato, Voix du Sahel. To amma a halin yanzu Nijar ta mallaki gidajen radiyo masu zaman kansu sama da 35 da radiyoyin raya karkara kimanin 134. Sai dai yanzu haka da dama daga cikin wadannan gidajan radiyo na fama da matsaloli daban daban.
Sau tari a cikin mafi yawancin gidajen radiyo masu a kasar ta Nijar. na fiskantar matsaloli sabili da matsalar rashin kayan aiki na gari. Sai dai a cewar Malam Shaibu Mamam sakatare janar na kungiyar masu gidajan radiyo da talabijin na kasar Nijar, yanzu haka akwai wasu jerin matsalolin da ke nan su na yin barazanar ga rayuwar gidajen radiyon a kasar ta Nijar.
Amma wannan biki na ranar radiyo ta duniya na bana, ya zo ma gidajen radiyon kasar ta Nijar a cikin mugun yanayi, a sakamakon kame-kamen 'yan jarida da hukumomin kasar su ka kaddamar, inda a cikin kasa da wata daya, 'yan jarida bakwai su ka tsinci kansu a hannun hukumar 'yan sanda ta kasa, a bisa zarginsu da aikata kuskuran alkalami. Kame-kamen da daraktan gidan radiyon Amfani Malam Gremah Bukar, ya ce sun sabawa dokokin Nijar dama alkawarin shugaban kasa Muohammadou Issoufou ya yi na cewa a zamanin mulkin sa ba za a kama dan jarida ko guda ba.
Saidai ko da ya ke har kawo yanzu wannan mataki na kame-kamen yan
jarida na gudana a birnin Yamai ne kawai, suma gidajen radiyo na cikin
kasa na fuskantar wani nau'in kalubalen da ke yin barazana ga aikin
nasu, a cewar Malam Harouna Mamane Bako, daraktan gidan radiyon Niyya Fm na birnin Konni.
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Usman Shehu Usman