An gudanar da taro tsakanin jami´an Amirka da na Iran a Bagadaza
May 28, 2007A karon farko cikin shekaru kusan 30 manyan jami´an gwamnatocin kasashen Amirka da Iran sun gudanar taro a game da halin da ake ciki a Iraqi. Wakilan kasashen biyu karkashin jagorancin jakadunsu sun tattauna ta tsawon sa´o´i 4 a yankin nan mai cike da tsaro na Green Zone dake birnin Bagadaza. Tun a cikin shekarar 1979 bayan juyin juya halin Islama a Iran, aka katse huldar diplomasiya tsakanin gwamnatocin biranen Teheran da Washington. Jakadan Amirka a Iraqi Ryan Crocker ya wakilci kasar sa yayin da jakadan Iran Hassan Kasemi Komi ya wakilci kasarsa a gun taron na yau. Crocker ya bayyana taron da cewa yayi armashi.
“Mun gabatarwa Iran damuwarmu game da take taken ta a Iraqi da goyon bayan da take bawa ´yan takife dake yakar dakarun Iraqi da na kawance. Mun fada musu cewar dole ne a daina tura makamai daga Iran zuwa Iraqi.”
Shi ma a nasa bangaren jakadan Iran ya tabbatar da ba da taimako wajen horas da jami´an tsaron Iraqi.