1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi masayar wuta a Yemen

Zulaiha Abubakar
December 26, 2018

Wakilan Majalisar Dinkin Duniya masu sanya ido a yarjejeniyar tsagaita wuta a Yemen sun gudanar da taron gaggawa tare da jami'an gwamnatin kasar a Hodeida bayan barkewar rikicin a makon da ya gabata.

UN Team Untersuchung Yemen
Hoto: Reuters/F. Salman

Yarjejeniyar sulhun a Hodeida da yankunan dake kusa da birnin ta fara aiki ne tun 18 ga wannan wata sai dai akwai shakku game da dorewar ta saboda yadda dukkan bangarorin biyu suke cigaba da nunawa juna yatsa. A wannan Larabar ce bangaren gwamnatin kasar masu goyon bayan kasar Saudiya su ka yi musayar wuta da 'yan tawayen Houthi masu goyon baya daga Iran arangamar da ta girgiza gabashin kasar. Yakin na kasar Yemen dai ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane sama da dubu 10 cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.

 

 

.