SiyasaSomaliya
Somaliland: Zaben shugaban kasa cikin tashin hankali
November 13, 2024Talla
Masu kada kuri'a miliyan miliyan daya da dubu 22 za su zabi tsakanin shugaban kasa mai barin gado,shugaban babbar jam'iyyar adawa Abdirahman Mohamed Abdullahi, da kuma shugaban jam'iyyar Social Justice Party (UCID) Faysal Ali Warabe. Tun farko an so shirya gudanar da zaben a shekara ta 2022, amma aka dageshi saboda dalilan rashin kudi. Amma 'yan adawa sun yi tir da lamarin kan cewar shugaban na neman tsawaita wa'adin mulkinsa