1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Amirka sun kashe Abu Bakr al-Baghdadi

Suleiman Babayo MAB
October 28, 2019

An halaka Abu Bakr al-Baghdadi jagoran kungiyar IS yayin wani farmaki na sojojin Amirka cikin wani yanki na kasar Siriya. Shugaba Donald Trump na Amikra ya tabbatar da cewa wannan harin ya halaka jagoran kungiyar IS.

Irak Abu Bakr al-Baghdadi
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Al-Furqan

Shugaba Donald Trump na Amirka yayin wani jawabi da ya yi ya tabbatar cewa dakarun kasarsa sun kai farmaki a yankin Arewa maso yammacin Siriya inda matakin ya kai ga mutuwar jagoran kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi.

Shugaba Donald Trump na Amirka ya bayar da umurnin kai farmakin da kashe jagoran Kungiyar ta IS Abu Bakr al-Baghdadi dan shekaru 48 da haihuwa haifaffen kasar Iraki. Shugaban na Amirkya ya yaba da hadin kai da ya samu daga sauran kasashen yayin farmakin.

Tun farko wani labari ya nuna cewa wata majiya daga kasar Siriya ta tabbatar wa mahukuntan Iraki cewa an kashe Abu Bakr al-Baghdadi jagoran kungiyar ta IS mai neman kafa daula na addinin Islama.