SiyasaAsiya
Tashin hankali na karuwa a Afghanistan
April 13, 2021Talla
Fiye da jami'an tsaron kasar Afghanistan 20 sun halaka cikin kwana guda sakamakon hare-hare cikin manyan larduna hudu na kasar. Hukumomi sun ce daga ciki akwai sojoji 10 da suka rasa rayukansu bisa harin 'yan kungiyar Taliban masu dauke da makamai.
Hare-haren na zuwa lokacin da Shugaba Ashraf Ghani ya bukaci 'yan Taliban su tsagaita wuta na rikicin da ke faruwa saboda azumin watan Ramadan da Musulmai suka fara a sassan duniya. Kasar ta Afghanistan tana ci gaba da samun kanta cikin tashe-tashe hankula masu nasaba da tsagerun Taliban da sauran kungiyoyi masu masu kaifin kishin Islama.