1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Taliban ta yi tir da harin da aka kai Kabul

August 26, 2021

Ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon ta tabbatar da afkuwar hare-hare guda biyu a gefen filin jirgin saman Kabul na Afghanistan. Mai magana da yawun Pentagon ya ce harin ya jikkata sojoji da fararen hula.

Afghanistan | Kabul Airport Explosion
Hoto: Wakil Kohsar/AFP/Getty Images

Kimanin mutane 13 ake fargabar hare-haren sun halaka a yayin da mutane 15 suka jikkata. Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin hare-haren.

Dama dai wasu kasashen yamma sun yi hasashen za a kaddamar da hari a kan filin jirgin saman, inda Jamus tuni ta sanar da dakatar da jigilar mutanen da take yi daga Afghanistan din. 

Sai dai kuma rahotannin na cewa  jami'an Amurka sun sake nuna zullumin yiwuwar sake kai hari a filin jirgin saman. To amma kungiyar Taliban ta yi Allah wadai da hare-haren da ta ce sun faru ne a yankin da Amurka ke da iko.