1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An halaka ´yan Taliban a Afghanistan

May 26, 2006

´Yan sandan Afghanistan sun halaka mutane 10 da ake zargi sojin sa kai ne na kungiyar Taliban bayan sun yiwa wata motar ´yan sanda kwantan bauna a tsakiyar kasar. Jami´an ´yan sanda sun ce an kashe abokin aikinsu daya a wannan hari wanda ya haddasa wata musayar wuta ta tsawon awa daya. An kai harin ne a lardin Ghazni mai nisan kilomita 150 kudu maso yammacin babban birnin kasar Kabul. A cikin kwanaki 10 da suka wuce an fuskanci fadace fadace mafi muni a cikin kasar ta Afghanistan tun bayan da dakarun kawance karkashin jagorancin Amirka suka hambarad da gwamnatin Taliban a karshen shekara ta 2001.