1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hallaka dakarun kiyaye zaman lafiya hudu a Sudan

October 3, 2012

Dakarun kiyaye zaman lafiya hudu sun hallaka yayin da takwas su ka samu raunika, sakamakon hari a Lardin Darfur na Sudan.

UNAMID peacekeeper Sergent Kindu Tarekegn, from Adigrat, Ethiopia, escorts a family that is returning home after farming outside Gereida (South Darfur) July 25, 2012. According to UNAMID, women, children and the elderly living in camps, in the government forces controlled Gereida, usually farm surrounding lands while men work in further areas in order to avoid robberies, rapes and other perpetrations. UNAMID added that in May, the rebel movement occupied Gereida for 24 hours after a big clash that destroyed telecommunication facilities and several buildings. UNAMID has deployed a battalion of more than 800 soldiers from Ethiopia for the protection of civilians. Picture taken July 25, 2012. REUTERS/Albert Gonzalez Farran/UNAMID/Handout (SUDAN - Tags: POLITICS MILITARY AGRICULTURE CONFLICT) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
UNAMID Darfur SudanHoto: Reuters

Wani harin kwanton ɓauna ya yi sanadiyar hallaka dakarun kiyaye zaman lafiya huɗu, na Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afrika, a Lardin Darfur na Yammacin ƙasar Sudan.

Rundinar ta ce an kai wannan hari cikin daren jiya Talata, yayin da dakarun Najeriya ke aikin sintiri, kuma akwai wasu dakarun takwas da su ka samu raunika.

Tuni shugaban dakarun kiyaye zaman lafiyar na Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afrika Lt Gen Patrick Nyamvumba, ya nemi mahukuntan birnin Khartoum su farauto maharan.

Tun cikin shekara ta 2003 bayan ƙazancewar lamuran ƙasar ta Sudan, aka tura dakarun na kiyaye zaman, kuma tun daga wannan lokaci kawo yanzu kimanin dakaru 42 su ka hallaka yayin neman wanzar da zaman lafiyar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu