An hallaka masallata 12 a Afghanistan
May 14, 2021Talla
Baya ga rasa na rayukkan da aka samu, harin ya kuma jikkata masallatan sama da 15 in ji mai magana da yawun rundunar yan sandan yankin Ferdous Faramarz, sai dai a cewarsa babu wanda ya dauki alhakin kai harin kawo yanzu.
Harin dai na yau din nan, na zuwa ne kasa da mako guda bayan kai wani harin da ya hallaka yara yan makaranta sama da 80 yan kabilar Hazara masu bin tafarkin shi'a wanda kungiyar Taliban ta nisanta kanta da harin. Kungiyar ta Taliban da ma can ta sanar da tsagaita wuta na kwanaki uku domin gudanar da bukukuwan sallah karama bayan kammala azumin watan Ramadana.