An hallaka sojojin NIjar masu yawa a sabon hari
September 12, 2025
Majiyoyi na cikin gida sun ce hare-hare guda biyu da aka kai a ranar Laraba ne suka janyo asarar rayukan sojojin da kuma 'yan sandan tsaron kasa.
Wani tsohon jami'i a yankin ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, cewa 'yan ta'adda sun kashe sojoji 20, yayin da wasu rahotanni ke nuna cewa adadin mutanen da suka mutu na iya zarta haka.
Karin bayani: 'Yan ta'adda sun kashe sojojin Nijar
Wannan yanki, wanda ke iyaka da Burkina Faso da Mali, ya dade yana zama mafaka ga kungiyoyin jihadi da ke da alaka da Al-Qaida da kuma ISIS.A halin da ake ciki, kungiyar kare hakkkin bil'Adama ta Human Rights Watch ta yi kira ga hukumomin Nijarda su kara kaimi wajen kare fararen hula a yankin Tillaberi, wandatun watan Maris na wannan shekara ke fama da hare-hare.