1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An hana bikin tunawa da Tiananmen

Ramatu Garba Baba
June 4, 2021

Hong Kong ta karfafa matakan tsaro domin hana duk wasu bukukuwa da aka saba yi don tunawa da ranar da aka tarwatsa wata zanga-zanga da aka yi a dandalin Tiananmen.

Archivbild I China I Tiananmen I Studentenproteste 1989
Hoto: AFP/picture alliance

Hukumomi a yankin Hong Kong sun karfafa matakan tsaro domin hana duk wasu bukukuwa da aka saba yi don tunawa da ranar da aka tarwatsa wata zanga-zanga da aka yi a dandalin nan na Tiananmen na birnin Beijing da ke kasar China, yau shekaru talatin da biyu da suka gabata kenan. Mahukuntan yankin sun kuma kama tare da tsare, Chow Hang Tung, wacce ta shirya jagorantar bikin.

Duk da hannin, wasu sun ci gaba da bikin raya ranar ta hanyar kunna kendura a tagogin gidajensu. Daukar matakin dai, ba ya rasa nasaba da yadda yankin na Hong Kong, ya sha fama da tashe-tashen hankula na masu adawa da kuma sukar lamirin gwamnatin yankin ba.

A dai shekara alif da dari tara da tamanin da tara ne, sojojin kasar China suka murkushe masu zanga-zangar neman kafa demokradiyya a dandalin na Tia-nanmen da ke birnin Beijing, inda dubbai suka rasa rayukansu, an ci gaba da cece-kuce kan wannan rana a tsakanin kasar ta China da makwabtanta bayan zargin mahukuntan na China da goge duk wani batu da ya shafi ranar a shafukan intanet.