1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawa da rundunar sojin Faransa

Ramatu Garba Baba
November 20, 2021

Masu zanga-zangar adawa da kasancewar sojojin Faransa a yankin Sahel ne suka tare hanya don hana rundunar shiga jamhuriyyar Nijar daga kasar Burkina Faso.

Mali Frankreich beendet die Operation „Barkhane“
Hoto: AP Photo/picture alliance

Shedun gani da ido sun bayar da labarin yadda dandazon jama'a suka yi kokarin dakatar da wani ayarin sojin Faransa da ke kokarin shiga Jamhuriyyar Nijar daga kasar Burkina Faso a yammancin jiya Juma'a. An dai ga yadda dandazon jama'a suka fito a wani jerin gwano tare da tare hanyar, don nuna adawa da rawar da Faransa ke takawa a rikicin yankin Sahel da sunan fada da mayaka masu ikirarin jihadi da suka hana zaman lafiya.

Mutanen na ganin kasancewar rundunar Faransa bata yi wani tasiri ba a maimakon hakan zamansu ya kara dagula lissafi ne a yakin da kasashen ke yi da ta'addanci, ganin yadda rashin kwanciyar hankali da hare-hare daga mayakan jihadin ke kara kamari. Faransa ta soma jibge dakarunta a Mali a shekara 2013 amma a baya-bayan nan tana fuskantar suka da kiran da kasashen Burkina Faso da Mali da jamhuriyyar Nijar da Mauritaniya da kuma Chadi suka yi don neman ta janye rundunar baki daya daga yankin.